Wednesday, July 4, 2007

Wakar Begen Muhammadu, ta Malam Nasiru Kabara.

Begen Muhammadu ya cikamini zuciya,

Acikinta ba sauran muhalli ko daya.



Wallahi garwashin bidarsa du da shi,

Ya k'ona sassan zuciya wayaniya.



Na so ka D'aha kamar ido ga makauniya,

Na so in je ni gare koda sau daya.



Na so ziyara ga ni ba ni da fuffuke,

K'ak'a ni kai in gano masoyin zuciya.



Na so ka san mai wabiya da ta so d'iya,

Koko muridhi yadda ya so lafiya.



Ko son abinci ga wanda ya yunwata,

Koko ruwa ga mai k'ishi da ya sha wuya.



Mukhtaru ka tafi ban ganka a duniya,

Ko na rabauta in ganka ko kun kwanciya.



Acikin mafarkin in na samu sai in ce,

Allahu Akbar u'uhu wayyoniya.



Begenka ya k'onan k'ashi har jijiya,

Naman jikina ya zagwanye bai d'aya.



Ya k'ona hanta har da hanji duka,

Ya bar hawayen zuciya da idaniya.



K'aunarka ta k'one buk'atar zuciya,

Sai ko ganinka da yammaci ko safiya.



Ta ya da zancen duniya tatsuniya

Ta dauki amri wanda ya zam gaskiya.



Ta ya da zancen zo-mu-ji-ta da kan fad'a,

Ta kalmashe gizo ta hana masa k'ok'iya.



Duka zuciyar da ta so ka D'aha da gaskiya,

Wallahi ta arzurta ba shauran tsiya.



Tai sitira ta tufata launi bam da bam,

La budda tai sha'ani irin na hawainiya.



Wata safiya tai murmushi wata safiya,

Riga fara wataran ta sawo shudiya.



Wataran da alkebba fara wataran ko,

Ya fashe da kuka ni a wa d'an saniya.



K'ak'a ni kai na bak'in cikin nan duniya,

Wa zan k'ara gunsa ne wayyo niya.



Ko na yi k'ara babu mai ji ko ya zam,

kukan amale ni ka yi ko jiniya.



Mukhtaru ya faku ga ganinsa yai wuya,

Belle in ce masa D'aha ni na sha wuya.



Shi ne abin k'ara gare shi gani na sa,

Ya zam kamar k'oyin farar hankakiya.



Da na san ganinsa yana da 'yar farkar wuya,

Na dauki jurewa ina ta dawainiya.



Dan babu wanda nake da shi zai taimakan,

Na sauke kayan zuciya sai d'uriya.



Na ce ganin maka abbukatar zuciya,

In dai na sami Wallah ya koran tsiya.



In je ni haifu minan isamguri na je,

In sha ruwan zam-zam inuta in kewaya.



In je safa in je ni marwa indawaya,

In je musallaci in jiranci mazan jiya.



Sannan in dawo in d'awafin sallama,

Bayan muk'amin nan da D'aha ya tsai tsaya.



In yo hajina kamili in masgaya,

Ni dai nufina gun mazajen gaskiya.



Ko da ina yin rarrafe in ja jiki,

In zo madina gurin Habibu abin biya.



In je ni raudhan nan ta D'aha in sunkuya,

In gaisuwa in biya bukatar zuciya.



Dan Anbiya nasa na kira ka rabbana,

Ka jikan masoyan D'aha yamma da safiya.



Ganar dani Mukhtari D'aha alaniya,

Domin ya koran duk jami'u shujuniya,



Dauke hijabi Rabba in gan shi fai,

Nan duniya ya Rabbi ko a manamiya.



Rahmarka ta gama kowanne balle niya,

Dana dauki k'arata ilaika Ilahiya.



Ya Rabbi nai kara gare ka fa kai daya,

Bayanka waye za ya amsa du'a'iya.



Kayyo Salati Rabbi gun mata nasa,

Kayo wata Rabbi gun sahabu da aliya.



Duk sanda mai bege ya ce k'ul safiya,

Sallu Alal Mukhtari koda sau daya.



Auk'ala zuttashd'iri fi takmilihi,

Begen Muhammadu ya cikamin zuciya.



2 comments:

Anonymous said...

Loved your site, Lee! Thanks for sharing Kami menyediakan berbagai macam obat seperti Obat kondiloma , Kencing Nanah , Wasir , Sipilis , Herpes , Diabetes

Unknown said...

I like prophet Muhammad saw
When I read all sirah I just get happened,may halp us we see Muhammad saw