Monday, July 9, 2007

Ta'alikin Wak'ar Damina. Daga BNG.

Tabaraka Allah mai iko,
Ranar da ba wani mai iko,
Mamallakin ran sakamako,
Kayi mu d'ai ba fifiko,
Nufinka ne Jalla Rabbana.

Wakar ga ta sa ni zulumi,
Ina ta tunani nai tagumi,
Na ji ta ni tun ina karami,
Ban manta ba cikin azumi
Isma'eel ke wakar damina

Shukuran ba na fahari,
Ni zuciyata duk tai fari,
Ina ta zogi ina marari,
Ina ta zumudin yin k'ari,
Acikin wakarnan ta damina.

'Yan baitukana babu yawa,
Wai motsi ya fi labewa,
Koda kana can cikin dawa,
Ga Zaki da Kura ga Giwa,
Tsiranka sai dai Jalla Rabbana.

Lallai an sha ruwan fari,
Duk Zuciyarmu tayi fari,
Albarka mai kauda fari,
Jalla kawar da dodon fari,
Ma su cinye amfani da damina.

Ga gaisuwa ta ga Na'ibi,
Nayi tane cikin ladabi,
Shafa ni na bar tararrabi,
Nayi rubutu babi-babi,
Rabbi kai nake wa rokona.

Anan nake so ni zan tsaya,
Mai ta'aliki ba gajiya,
BNG mai karafkiya,
Lalube nake neman hanya,
Acikin duhun daren damina.

No comments: