Bismilla Allah Madawwami,
Shi Mahaliccinmu Rahimi,
Mai yawaita alheri magami,
Wanda ya yi rani da damina.
Komai yana yi mai ma'ana,
Don hikimominsa Rabbana,
Masu yawa ko a ko ina,
Tabaraka Sarkin sarakuna,
Ya sa ni'imomi ga damina.
Nomau manomi mai dariya,
Tsaya inai maka tambaya,
Shin me yake ba ka dariya,
Ko kana da jikkar zinariya,
Ko ko ka ci riba da damina.
Sai ya kada baki da hamzari,
Ya ce da ni kai albishiri,
Yau zuciyata ta yi fari,
Zak'inta ya zarce sukari,
Na ga malama ta damina.
D'ago kai ka dubo samaniya,
Ka ga gajimarai na tafiya,
Kafin na bushe da dariya,
Sai na ji tsawa da walkiya,
Suna bushara ga damina.
Nan da nan gari ya fitittike,
Kamar girar sa a murtuke,
Wanda aka d'aure jikin turke,
To nan da nan sai mun ka fake,
Don gudun jik'ewa ga damina.
Sai cida ka ke ji cikin gari,
Sama tayi damkam sai hadari,
Tafiya yake yi da hanzari,
Kamar ana kora ayari,
Hauragiya sai su damina.
In ka ga haske da walkiya,
Kamar wutar Yola tunniya,
Sararin sama na rugunniya,
Kamar maza na hayaniya,
Nam'an wa haufan ga damina.
Za ka ga iska da guguwa,
Suna ta shara da kokawa,
Suna busharar akwai ruwa,
Kowa ya shirya yana zuwa,
Mu ne ma'aikata na damina.
Ku masu shanya ku tattara,
Ko ku masu murhu ku ciccira,
Kafin ka ce ga bakin zare,
Sai ruwa ya tsuge cikin dare,
Ya nuna halinta damina.
Ruwa ya kwana guna-guna,
Kamar ana yi da guguna,
Sai kankara ga ta ko ana,
Allah jikan wasu d'akuna,
Yau damina ta yi damina.
Abin sha'awa sai da jijjifi,
Ko ana ka duba kamar afi,
Ka ga mutane ba lissafi,
Gonarsa kowa yakan tafi,
Da iri ya shuka da damina.
Kan a jima ko a ko'ana,
Gud'a ka ke ji da ganguna,
Yau fa manoma kamar dina,
Sai jefa garma da jinina,
Ayyuriri mu na damina.
Kwana kadan kungi yawuwa,
Gyada da dawa da yakuwa,
Duk sun yi kore gwanin k'awa,
Dukan yabanya sai yad'uwa,
Saboda danshi na damina.
Sai kurum a ran nan da safiya,
Nomau ya b'ullo da dariya,
Ya ce dani za shi gewaya,
Nan take sai muka rankaya,
Muna bushara ga damina.
Dawa da gero sai rangwad'a,
Kamar amare gidan kid'a,
Sannan da dubo wajen gyad'a,
Sai na ganta shar-shar tana fad'a,
Na gode aikinki damina.
Daga nan na jiya ga auduga,
Duk inda na hango ta sai na ga,
Sai dariya ba k'ididdiga,
Kai, fara'a sai su auduga,
Saboda tsarinta damina.
Sai muka koma da murmushi,
Ya bud'e baki da dasashi,
Kamar da d'ai ba shi yin fushi,
Yana fad'in "duk mai karfi"
Za ya sami kud'i da damina.
Ran da za'a girbi kamar buki,
Kowa da lauje suke jiki,
Kan a jima babu ko haki,
An daure damai daki-daki,
Ka ji hukuncinta damina.
Kai a takaice in ce da kai,
Sai na ga jakai akai akai,
Suna jido sai su zo su kai,
Buhu da dammai har masakai,
Albarkaci ne na damina,
Kaka uwa ce ga damina,
Idan ta bullo a ko ina,
Za ka ga manya da kankana,
Suna ta harka da kunbuna,
Saboda innarmu damina.
Tun daga k'auye ka ke gani,
Kowa ne babba da kankani,
Harkarsu sai wanda ya sani,
Mata ko sai kirma a zani,
Saboda kaka ta damina.
Haukan su nomau na dayawa,
Wai sun ga kudi na samuwa,
Aure suke yi babu haihuwa,
A kai a kai ka yi faduwa,
Da watsa ni'ima ta damina.
Manyan samari da kankana,
Sai taguwoyi da riguna,
Ga jakuna nan da dokuna,
Wasunsu har ma da kekuna,
Bore suke yi wa damina.
Nan na ga shanu na ta dara,
Ywansu wane d'ari tara,
Sun yi k'iba duk ga madara,
Sun sami d'anya suna ta cira,
Sun ci harawa ta damina.
Kai a tak'aice ko ka jiya,
Komai ka duba ko bishiya,
Za ka ga ta sake rausaya,
Kamar amarya ko gimbiya,
kowa gada ta sa damina.
Kai direba mai giwa a dawa,
Ina ka b'ullo na zuwa,
Ko lafiya Sarkin sukuwa?
Na ga gudun naka yai yawa,
Ga sh kuwa mun zarce damina.
Sai ya ce da ni hanga ka gani,
Ka san sukuwa sai mutum gwani,
Shi dai ya ka yi ba ya lahani,
Dalar gyada an kace da ni,
Nai ta jido wa da damina.
Daga zuwa na cikin gari,
Sai k'ungiyoyi d'ari-d'ari,
Suna ta aiki da hamzari,
Wassu suna kan basukuri,
Albarkacin gwaggo damina.
Idan duk ka duba a ko ana,
Babur da mota da kekuna,
Kamar gafiyoyi a titina,
Su yi kasuwa su yi kantuna,
Kowa busy sai su damina.
Yaran gari ko sai bal suke,
Kowa ka duba very happy,
Da damina dai mutum take,
Da an mutum sai son a sake,
Ka ji suffofinta damina.
In da mutum ce ba garari,
Da an mutum mai halin gari,
Kogina baiwa ba had'ari,
Mai mai da dukkan bak'i fari,
Mai fara'a ka ji damina.
Mai dariya mai son shagali,
Ko ya yi fad'a wani sa'ili,
Sai ka ce da shi sannu adali,
Kyautarka ta zarce misali,
Allah ya bar mana damina.
Kaka uwar yalwatar gari,
Da mace ce za'ai ta gari,
Mai baiwa jikokinta d'ari,
Ta sha da su nonon sukari,
Kaka uwar inna damina.
Na gode Allah Ubangiji,
Wanda ya ba ni gani da ji,
Ya ba ni tunani aji-aji,
Tabaraka na rok'i agaji,
Ka ba ni hazzi da damina.
Mai tambaya in ka so ka bi,
Suna na yanka ko lak'abi
Ce Adamu ko ko Na'ibi,
Wali Sulaimanu ne Abi,
Wanda ya wawwak'e damina.
Alhamdulillahi a gama,
Na kama doki mai ragama,
Na yi tab'i na yi tak'ama,
Na sauka ba wata gardama,
Saboda kaka da damina.
Muna salati ga Annabi,
Muhammadu wanda mu ke ta bi,
Kazalika Alu da Sahhabi,
Da Auliya'u da masu bi,
Baiwarsu ta zarce damina.
Saturday, July 7, 2007
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
3 comments:
Wannan wakar tayi tun muna firamare Muke jinta har yanzu kuma,Allah ya Saka da alkairi
Ina ta nemanta tin a primary sai yau. Ina godiya sosai
Alhamdulillah najima ina neman wakar nan sai yau nasamu. Allah ya saka da alkhairi Allah yajikan Malam Naibi Suleiman Wali
Post a Comment