Na tuba na bi Ubangiji,
Na daina aikin munkari.
Na kama turbar Annabi,
Gwadabe mikakke D'ahiri.
Na tabbata da Ubangiji daya ne,
A b'oye da zahiri,
Na kama hanyar shugaban,
Duka sayyadi Abdulk'adiri.
Na jure cutar d'an Adam,
Domin na tabbata ankuri.
Na dena zagin dan Adam,
Balle in ce masa kafiri.
Na tuba ni na bar kula,
Da makangara a cikin gari.
Na dena Sallah ni kad'an,
Na bar k'awar duka ja'iri.
Sallah cikin jama'ar masallaci,
Adan Alamajiri.
Duka wanda ya zage ni,
Kai masa gafara Ya Gafiri.
Zikiri a kowanne lokaci,
Safe da yamma da daddare.
Shi ne abinci na da shi,
Aka sanni du a cikin gari.
Aljanna na hannun iyaye,
Na rok'e su sunadari.
Na roki Jalla Ubangiji,
Ya tsare ni aikin munkari.
Na yo salati da salama,
A gurin Muhammadu D'ahiri.
Ya Rabbi kai mana gafara,
Don sayyadi Abdulkadiri.
Insha Allahu daga lokaci zuwa lokaci zan dinga sako wakokin Malamin, domin su ba zu a ko'ina, a haka ne jama'a za su karu da hikimomin da Allah ya horewa Malamin.
Friday, June 29, 2007
Subscribe to:
Posts (Atom)